Skip to content

Ayoyin Littafi Mai Tsarki game da Union

5 ayoyi · 1 fanni

Mahimman ayoyin Littafi Mai Tsarki

  1. Shirye-shirye sukan lalace saboda rashin neman shawara, amma tare da mashawarta masu yawa za su yi nasara.

  2. Biyu sun fi ɗaya, gama suna samun riba mai kyau na aikinsu.

  3. In ɗaya ya fāɗi, abokinsa zai taimake shi yă tashi. Amma abin tausayi ne ga mutumin da ya fāɗi ba shi kuma da wanda zai taimake shi yă tashi!

  4. In mutum biyu sun kwanta tare, za su ji ɗumin juna. Amma yaya mutum ɗaya zai ji ɗumi yana shi kaɗai?

  5. Ana iya shan ƙarfin mutum ɗaya, mutum biyu za su iya kāre kansu. Igiya riɓi uku tana da wuya tsinkawa.