Tsallake zuwa abun ciki

Ayoyin Littafi Mai Tsarki game da The Daily Sacrifice

8 ayoyi · 13 fannoni

Mahimman ayoyin Littafi Mai Tsarki

  1. “Ka ba Haruna da ’ya’yansa maza wannan umarni, ‘Waɗannan su ne ƙa’idodi don hadaya ta ƙonawa. Hadaya ta ƙonawa za tă kasance a bagade dukan dare, sai da safe, kuma dole a bar wutar tă yi ta ci a bisa bagaden.

  2. Sa’an nan firist zai sa rigunarsa ta lilin da kuma rigar lilin da ake sa a ciki, sa’an nan yă kwashe tokan hadaya ta ƙonawa da wuta da ta ci a kan bagaden, yă sa kusa da bagaden.

  3. Sa’an nan yă tuɓe waɗannan rigunan yă sa waɗansu, sa’an nan yă ɗauki tokar yă kai waje da sansani zuwa inda yake da tsabta.

  4. Dole a bar wutar da take bisa bagaden tă yi ta ci; kada tă mutu. Kowace safiya firist zai ƙara itacen wuta, yă shirya hadaya ta ƙonawa a bisa wutar yă kuma ƙone kitsen hadaya ta salama a kansa.

  5. tare da hadaya ta lallausan gari kashi ɗaya bisa goma na efan, kwaɓaɓɓe da kwalaba ɗaya na man zaitun mafi kyau.

  6. Wannan ita ce hadaya ta ƙonawa ta kullum wadda aka kafa a Dutsen Sinai, don daɗin ƙanshi, wato, hadaya ce da aka ƙone da wuta ga Ubangiji.

  7. Hadaya ta sha, za tă zama kwalaba ɗaya na ruwan inabi, da ɗan rago guda. Za a kwarara hadaya ta sha ga Ubangiji a wuri mai tsarki.

  8. Ɗayan ɗan ragon kuma za a miƙa shi da yamma, tare irin hadaya ta lallausan gari, da hadaya ta sha da ka yi da safe. Wannan hadaya ce ta ƙonawa mai daɗin ƙanshi ga Ubangiji.