Skip to content

Ayoyin Littafi Mai Tsarki game da The Cedar

8 ayoyi · 30 fannoni

Mahimman ayoyin Littafi Mai Tsarki

  1. firist zai umarta a kawo tsuntsaye biyu masu rai, masu tsabta da itacen al’ul, jan ƙyalle da kuma hizzob saboda mutumin da za a tsabtacce.

  2. Sa’an nan firist zai umarta a kashe ɗaya daga cikin tsuntsayen a bisa ruwa mai kyau a tukunyar laka.

  3. Zai ɗauki tsuntsu mai rai ya tsoma shi tare da itacen al’ul, jan ƙyalle da kuma hizzob cikin jinin tsuntsun da aka yanka a bisa ruwa mai kyau.

  4. Sau bakwai zai yayyafa wa mutumin da za a tsabtacce daga cutar mai yaɗuwa ya kuma furta shi tsarkakakke. Sa’an nan ya saki tsuntsu mai rai ɗin ya tafi.

  5. Don a tsabtacce gidan, zai ɗauki tsuntsaye biyu da itacen al’ul, jan ƙyalle da hizzob.

  6. Zai yanka ɗaya daga cikin tsuntsayen a bisa ruwa mai kyau a cikin tukunyar laka.

  7. Sa’an nan zai ɗauki itacen al’ul, hizzob, jan ƙyalle da kuma tsuntsu mai ran ya tsoma su cikin jinin tsuntsun da aka yanka da kuma cikin ruwa mai kyau, ya yayyafa wa gida sau bakwai.

  8. Zai tsabtacce gidan da jinin tsuntsun, ruwa mai kyau, tsuntsu mai ran, itacen al’ul, hizzob da kuma jan ƙyalle.