Skip to content

Ayoyin Littafi Mai Tsarki game da Tailoring

5 ayoyi

Mahimman ayoyin Littafi Mai Tsarki

  1. “Duba, na zaɓi Bezalel ɗan Uri, ɗan Hur, na kabilar Yahuda,

  2. na kuma cika shi da Ruhun Allah, fasaha, azanci, da kuma sani cikin kowace irin sana’a,

  3. Ban da haka, na zaɓi Oholiyab ɗan Ahisamak, na kabilar Dan, don yă taimake shi. Na kuma ba da fasaha ga dukan masu aikin sana’ar hannu, don yin duk abin da na umarce ka.

  4. da kuma saƙaƙƙun riguna, tsarkakan riguna don Haruna firist da rigunan ’ya’yansa maza, sa’ad da suke hidima a matsayin firistoci,

  5. Daga zare mai ruwan shuɗi, da shuɗayya da kuma jan zare suka yi tsarkaken rigunan domin hidima a wuri mai tsarki. Suka kuma yi tsarkaken riguna don Haruna, yadda Ubangiji ya umarci Musa.