Ayoyin Littafi Mai Tsarki game da Table: Figurative
Ayoyi game da Figurative
Kada ka bar ƙauna da aminci su rabu da kai; ka ɗaura su kewaye da wuyanka, ka rubuta su a allon zuciyarka.
“An rubuta zunubin Yahuda da alƙalamin ƙarfe, an rubuta da tsinin dutse, a kan allunan zukatansu da kuma a kan ƙahonin bagadansu.
Kun nuna cewa ku wasiƙa ce daga Kiristi, sakamakon hidimarmu, ba wadda aka rubuta da inki ba, sai dai da Ruhun Allah mai rai. Ba kuma a kan allunan dutse ba, sai dai a kan allunan zukatan mutane.