Ayoyin Littafi Mai Tsarki game da Statecraft: School in
Ayoyi game da School in
Sa’an nan sarkin ya umarci Ashfenaz, shugaban fadarsa yă kawo waɗansu daga cikin Isra’ilawan da suka fito daga gidan sarauta da kuma na fitattun mutane.
Matasa maza waɗanda ba su da wata naƙasa kuma kyawawa, hazikai ta kowace hanyar koyo, sanannu, masu saurin fahimtar abu, da kuma waɗanda suka cancanci su yi aiki a fadar sarki. Zai koya musu harshen Babiloniyawa da kuma littattafansu.
Sarki kuma ya sa a ba su abinci da ruwan inabi kowace rana daga cikin abincin sarki. Za a koyar da su har shekaru uku, bayan haka kuma su shiga yin wa sarki hidima.