Skip to content

Ayoyin Littafi Mai Tsarki game da Scapegoat

19 ayoyi

Mahimman ayoyin Littafi Mai Tsarki

  1. Sa’an nan zai ɗauki bunsurai biyu yă miƙa su a gaban Ubangiji a ƙofar Tentin Sujada.

  2. Haruna zai jefa ƙuri’a don awaki biyun ɗin, ƙuri’a ɗaya domin Ubangiji, ɗayan kuma don azazel

  3. Haruna zai kawo akuyar da ƙuri’a ta fāɗi a kai wa Ubangiji yă miƙa ta na hadaya don zunubi.

  4. Amma za a miƙa akuyar da aka zaɓa ta wurin ƙuri’a a matsayi ta azazel da rai a gaban Ubangiji don a yi amfani da ita don kafara ta wurin korinta zuwa cikin jeji kamar azazel.

  5. “Sa’ad da Haruna ya gama yin kafara domin Wuri Mafi Tsarki, Tentin Sujada da kuma bagade, sai yă kawo akuya mai rai.

  6. Haruna zai ɗibiya hannuwansa a kan akuya mai ran, yă furta a kansa dukan mugunta da tawayen Isra’ilawa, dukan zunubansu, yă kuma sa su a kan akuyan. Zai kori akuyan zuwa cikin jeji a hannun mutumin da aka ba shi aikin yin haka.

  7. Akuyan zai ɗauka a kansa dukan zunubansu zuwa kaɗaitaccen wuri, a can mutumin zai sake shi a jeji.

  8. “Sa’an nan Haruna zai shiga Tentin Sujada yă tuɓe rigunansa na lilin da ya sa, kafin yă shiga Wuri Mafi Tsarki, zai kuma bar su a can.

  9. Zai yi wanka a tsattsarkan wuri yă sa rigunarsa na kullum. Sa’an nan zai fita yă miƙa hadaya ta ƙonawa domin kansa da hadaya ta ƙonawa domin mutane, don yă yi kafara domin kansa da kuma domin mutane.

  10. Zai kuma ƙone kitsen hadaya don zunubi a kan bagade.

  11. “Dole mutumin da ya saki akuya na azazel yă wanke rigunansa yă kuma yi wanka; bayan haka zai iya shiga sansani.

  12. Dole a ɗauki jini, fata, nama da kuma ƙashin bijimi da akuyan hadaya don zunubi, waɗanda aka kawo jininsu cikin Wuri Mafi Tsarki don kafara, a kai waje da sansani a ƙone.

  13. Dole mutumin da ya ƙone su yă wanke rigunansa yă kuma yi wanka, bayan haka zai iya shiga sansani.

  14. “Wannan za tă zama dawwammamiyar farilla a gare ku. A rana ta goma ga wata na bakwai, dole ku yi mūsu kanku, ba kuwa za ku yi wani aiki ba, ko da mutum baƙo ne a cikinku ko kuwa ɗan ƙasa,

  15. gama a wannan rana za a yi kafara dominku, don a tsarkake ku. Sa’an nan a gaban Ubangiji, za a tsarkake ku daga dukan zunubanku.

  16. Asabbaci ne don hutawa, kuma dole ku yi mūsun kanku; wannan dawwammamiyar farilla ce.

  17. Firist da aka keɓe aka kuma naɗa don yă gāji mahaifinsa a matsayin babban firist ne zai yi kafara. Zai sa rigunan lilin masu tsarki

  18. yă yi kafara domin Wuri Mafi Tsarki, Tentin Sujada da bagade, da kuma saboda firistoci da kuma dukan jama’ar Isra’ila.

  19. “Wannan za tă zama dawwammamiyar farilla ce gare ku. Za a riƙa yin kafara sau ɗaya a shekara saboda dukan zunuban Isra’ilawa.” Aka kuma yi haka, yadda Ubangiji ya umarci Musa.