Ayoyin Littafi Mai Tsarki game da Keturah
Mahimman ayoyin Littafi Mai Tsarki
Ibrahim ya auro wata mace, mai suna Ketura.
Ta haifa masa Zimran, Yokshan, Medan, Midiyan, Ishbak da Shuwa.
Yokshan shi ne mahaifin Sheba da Dedan. Zuriyar Dedan su ne mutanen Ashur, da mutanen Letush, da kuma mutanen Lewummin.
’Ya’yan Midiyan maza su ne, Efa, Efer, Hanok, Abida, da kuma Elda’a. Dukan waɗannan zuriyar Ketura ce.