Skip to content

Ayoyin Littafi Mai Tsarki game da Insects

5 ayoyi · 23 fannoni

Mahimman ayoyin Littafi Mai Tsarki

  1. Sai dai akwai ƙwarin da suke da fikafikai masu tafiya da ƙafafu huɗu da za ku ci; waɗanda suke da cinyoyin da suke sa su iya tsalle.

  2. Za ku iya cin kowane irin fāra, gyare, ƙwanso da danginsu.

  3. Amma sauran ƙananan ƙwari duka masu fikafikai, suna kuma jan ciki, abin ƙyama ne a gare ku.

  4. “ ‘Duk wanda ya taɓa mushen waɗannan dabbobi, zai ƙazantu har fāɗuwar rana.

  5. Duk wanda ya ɗauki ɗaya daga cikin gawawwakinsu dole yă wanke rigunansa, zai kuma ƙazantu har zuwa yamma.