Skip to content

Ayoyin Littafi Mai Tsarki game da Iconoclasm

6 ayoyi · 1 fanni

Mahimman ayoyin Littafi Mai Tsarki

  1. Ku ƙone siffar allolinsu da wuta. Kada ku yi ƙyashin azurfa ko zinariyar da aka rufe allolin da ita, Kada ku kwashe su, don kada su zamar muku tarko, gama abin ƙyama ne ga Ubangiji Allahnku.

  2. Kada ku kawo abin ƙyama cikin gidajenku, domin kada ku zama kamar su. Gaba ɗaya ku yi ƙyamarsu, ku ƙi su, gama an ware su, sun zama domin a hallaka.

  3. Waɗannan su ne ƙa’idodi da kuma dokokin da za ku lura, ku kuma kiyaye a ƙasar da Ubangiji, Allahn kakanninku, yake ba ku don ku ci gādonta, muddin kuna zama a ƙasar.

  4. Ku hallaka dukan wuraren da al’umman da kuke kora suke yi wa allolinsu sujada, a kan duwatsu masu tsawo, da a kan tuddai, da kuma ƙarƙashin kowane itace gaba ɗaya.

  5. Ku rurrushe bagadansu, ku farfashe keɓaɓɓun duwatsunsu, ku kuma ƙone ginshiƙan Asheransu da wuta; ku yayyanka gumakan allolinsu, ku kuma shafe sunayensu daga waɗannan wurare.

  6. Ba za ku yi wa Ubangiji Allahnku sujada a hanyar da suke yi ba.