Ayoyin Littafi Mai Tsarki game da Good Children: Shall be blessed
Ayoyi game da Shall be blessed
Ɗana, kada ka manta da koyarwata, amma ka kiyaye umarnaina a cikin zuciyarka,
gama za su ƙara maka tsawon rai da shekaru masu yawa su kuma kawo maka wadata.
Kada ka bar ƙauna da aminci su rabu da kai; ka ɗaura su kewaye da wuyanka, ka rubuta su a allon zuciyarka.
Sa’an nan za ka sami tagomashi da kuma suna mai kyau a gaban Allah da kuma a gaban mutane.