Tsallake zuwa abun ciki

Ayoyin Littafi Mai Tsarki game da False Witness: General references

15 ayoyi · 1 fanni

Ayoyi game da General references

  1. “ ‘Kada ku yi sata. “ ‘Kada ku yi ƙarya. “ ‘Kada ku ruɗe juna.

  2. “ ‘Kada ku rantse bisa ƙarya da sunana, ta haka har ku ƙasƙantar da sunan Allahnku. Ni ne Ubangiji.

  3. In wani ɗan sharri ya tashi ya yi wa wani sharri, don a sami wani da laifi,

  4. dole mutanen nan biyu da suke rikici su tsaya a gaban Ubangiji, a gaban firistoci da alƙalai waɗanda suke aiki a lokacin.

  5. Dole alƙalan su yi bincike sosai, in kuma aka tabbatar mai ba da shaida maƙaryaci ne, yana ba da shaidar zur a kan ɗan’uwansa ne,

  6. to, sai a yi da shi yadda ya yi niyya yă yi da ɗan’uwansa. Dole ku fid da mugu daga cikinku.

  7. Sauran mutane za su ji wannan su kuma ji tsoro, ba kuwa za a ƙara yin irin wannan mugun abu a cikinku ba.

  8. Akwai abubuwa shida da Ubangiji ya ƙi, abubuwa bakwai da suke abin ƙyama gare shi,

  9. duban reni, harshe mai ƙarya, hannuwa masu zub da jinin marar laifi,

  10. zuciyar da take ƙulla mugayen dabaru, ƙafafun da suke sauri zuwa aikata mugunta,

  11. mai shaidar ƙarya wanda yake zuba ƙarairayi, da kuma mutumin da yake tā-da-na-zaune-tsaye a cikin ’yan’uwa.

  12. Sai ya ce mini, “Wannan ce la’anar da za tă ratsa dukan ƙasar; gama bisa ga abin da ya ce a gefe ɗaya, za a kawar da kowane ɓarawo, kuma bisa ga abin da ya ce a ɗaya gefen za a kawar da duk mai rantsuwar ƙarya.

  13. Ubangiji Maɗaukaki ya ce, ‘Zan aika shi, zai shiga gidan ɓarawo, da gidan mai rantsuwar ƙarya da sunana. Zai kasance a gidansa yă hallaka gidan da katakon da duwatsun.’ ”

  14. Mun kuma san cewa an yi doka ba domin masu adalci ba sai dai masu tawaye, da marasa biyayya, da marasa bin Allah, da masu zunubi, da marasa tsarkaka, da masu saɓon Allah, da masu kashe iyaye maza da mata, da masu kisankai,

  15. da masu zina da kuma da maza masu kwana da maza, ko mata masu kwana da mata, da masu cinikin bayi da masu ƙarya da kuma masu shaidar ƙarya, da kuma duk wani abin da ya saɓa wa sahihiyar koyarwa,