Skip to content

Ayoyin Littafi Mai Tsarki game da Cud

12 ayoyi · 1 fanni

Mahimman ayoyin Littafi Mai Tsarki

  1. Za ku iya cin dabbobin da suke da rababben kofato, waɗanda suke kuma tuƙa.

  2. “ ‘Akwai waɗanda suke tuƙa ko kuwa suna da rababben kofato kawai, duk da haka ba za ku ci su ba. Waɗannan kuwa su ne, raƙumi, ko da yake yana tuƙa, amma ba shi da rababben kofato; saboda haka cin namansa haram ne gare ku.

  3. Rema, ko da yake tana tuƙa, duk da haka ba ta da rababben kofato; saboda haka namanta haram ne gare ku.

  4. Zomo, ko da yake yana tuƙa, duk da haka ba shi da rababben kofato; saboda haka namansa haram ne gare ku.

  5. Alade, ko da yake yana da rababben kofato, amma ba ya tuƙa, saboda haka namansa haram ne gare ku.

  6. Ba za ku ci namansu ba, ko ku taɓa gawawwakinsu, gama haram ne gare ku.

  7. Kada ku ci wani haramtaccen abu.

  8. Waɗannan su ne dabbobin da za ku iya ci, saniya, tunkiya, akuya,

  9. mariri, barewa, mariya, makwarna, mazo, gada da kuma tunkiyar dutse.

  10. Za ku iya cin duk dabbar da take da rababben kofato, wadda kuma take sāke tona abin da suka riga suka haɗiye.

  11. Amma, cikin waɗanda suke sāke tona abin da suka riga suka haɗiye ɗin, ko suke da rababben kofato, ba za ku ci raƙumi, zomo ko rema ba. Ko da yake suna sāke tona abin da suka riga suka haɗiye, suna kuma da rababben kofato, su ɗin marar tsarki ne gare ku.

  12. Alade ma marar tsarki ne; ko da yake yana da rababben kofato, shi ba ya sāke tona abin da ya riga ya haɗiye. Ba za ku ci namansu ko ku taɓa gawarsu ba.