Ayoyin Littafi Mai Tsarki game da Charity
Mahimman ayoyin Littafi Mai Tsarki
Ƙauna tana da haƙuri, ƙauna tana da kirki. Ba ta kishi, ba ta burga, ba ta da girman kai.
Ba ta rashin ladabi, ba ta sonkai, ba ta da saurin fushi, ba ta riƙe mutum a zuciya.
Ƙauna ba ta jin daɗin mugunta, sai dai ta ji daɗin gaskiya.
Tana kāriya kullum, tana amincewa kullum, tana bege kullum, tana jimrewa kullum.