Skip to content

Ayoyin Littafi Mai Tsarki game da Bishop

13 ayoyi · 2 fannoni

Mahimman ayoyin Littafi Mai Tsarki

  1. To, dole mai kula da Ikkilisiya yă kasance marar abin zargi, mijin mace guda, mai sauƙinkai, mai kamunkai, wanda ake girmama, mai karɓan baƙi, mai iya koyarwa,

  2. ba mai buguwa ba, ba mai rikici ba sai dai mai hankali, ba mai yawan faɗa ba, ba kuma mai yawan son kuɗi ba.

  3. Dole yă iya tafiyar da iyalinsa da kyau, yă kuma tabbata cewa ’ya’yansa suna yin masa biyayya da ladabin da ya dace.

  4. (In mutum bai san yadda zai tafiyar da iyalinsa ba, yaya zai iya kula da ikkilisiyar Allah?)

  5. Kada yă zama sabon tuba, in ba haka zai zama mai girman kai yă kuma fāɗa cikin irin hukuncin da ya fāɗo wa Iblis.

  6. Dole kuma yă kasance da shaida mai kyau ga waɗanda suke na waje, don kada yă zama abin kunya yă kuma fāɗa cikin tarkon Iblis.

  7. Dalilin da ya sa na bar ka a Kirit shi ne don ka daidaita abubuwan da suka rage da ba a kammala ba, ka kuma naɗa dattawa a kowane gari, yadda na umarce ka.

  8. Dole dattijo yă kasance marar aibi, mijin mace guda, mutumin da ’ya’yansa masu bi ne, waɗanda kuma ba a san su da lalata ko rashin biyayya ba.

  9. Da yake an danƙa wa mai kula da ikkilisiya riƙon amana saboda Allah, dole yă zama marar aibi ba mai girman kai ba, ba mai saurin fushi ba, ba mai buguwa ba, ba mai rikici ba, ba kuma mai son ƙazamar riba ba.

  10. A maimakon haka dole yă zama mai karɓan baƙi, mai son abu nagari, mai kamunkai, mai adalci, mai tsarki da kuma natsattse.

  11. Dole yă riƙe tabbataccen saƙon nan kam-kam yadda aka koyar, don yă iya ƙarfafa waɗansu da sahihiyar koyarwa yă kuma ƙaryata waɗanda suke gāba da shi.

  12. Gama akwai ’yan tawaye da yawa, masu surutun banza da masu ruɗi, musamman ƙungiyar masu kaciya.

  13. Dole a hana su yin magana, domin suna kawo rushewar iyalai ta wurin koyar da abubuwan da bai kamata su koyar ba don neman ƙazamar riba.