Ayoyin Littafi Mai Tsarki game da Birthright: Belonged to the firstborn
Ayoyi game da Belonged to the firstborn
In mutum yana da mata biyu, yana kuwa ƙaunar ɗaya, ba ya kuma ƙaunar ɗayan, su biyun kuwa suka haifi masa ’ya’ya maza, sai ya zamana cewa ɗan farin ya kasance na wadda ba ya ƙauna,
to, a ranar da zai yi faɗa wane ne a cikin ’ya’yansa zai riƙe gādon da zai bar musu, kada yă sa ɗan matar da yake ƙauna yă zama kamar shi ne ɗan fari, a maimakon ɗan matar da ba ya ƙauna, wanda shi ne ɗan farin.