Skip to content

Ayoyin Littafi Mai Tsarki game da Ax

6 ayoyi · 4 fannoni

Mahimman ayoyin Littafi Mai Tsarki

  1. Saboda haka dukan Isra’ila sukan gangara zuwa wajen Filistiyawa domin su gyara bakin garemaninsu, da fartanansu, da gaturansu, da kuma laujunansu.

  2. Duk lokacin da za su gyara bakin garmansu da fartanyarsu sai sun biya tsabar azurfa biyu. Haka ma idan za su gyara gatari ko bakunan abin korar shanun noma sai sun biya tsabar azurfa ɗaya.

  3. Yayinda ɗayansu yake cikin saran itace, sai kan gatarin ya fāɗi a ruwa, sai ya ce, “Kash, ranka yă daɗe, kayan aro ne fa!”

  4. Sai mutumin Allah ya ce, “Daidai ina ya fāɗa?” Da ya nuna masa wurin, sai Elisha ya yanka ɗan sanda ya jefa a wurin, ya sa kan gatarin ya taso sama.

  5. Sun yi kamar mutane masu wāshin gatura don yanka itatuwa a kurmi.

  6. Sun ragargaje dukan sassaƙar katako da gatura da kuma gudumarsu.