Ayoyin Littafi Mai Tsarki game da Arm
Mahimman ayoyin Littafi Mai Tsarki
Duba, Ubangiji Mai Iko Duka yana zuwa da iko, hannunsa kuma yana yin mulki dominsa. Duba, ladarsa tana tare da shi, sakamakonsa kuma na rakiyarsa.
Yakan lura da garkensa kamar makiyayi. Yakan tattara tumaki wuri ɗaya yă riƙe su kurkusa da ƙirjinsa; a hankali kuma yakan bi da masu ba da mama.