Skip to content

Ayoyin Littafi Mai Tsarki game da Anointing Oil

7 ayoyi · 1 fanni

Mahimman ayoyin Littafi Mai Tsarki

  1. Sa’an nan Ubangiji ya ce wa Musa,

  2. “Ka ɗauki waɗannan kayan yaji masu kyau, shekel 500 na ruwan mur, rabin turaren sinnamon mai daɗin ƙanshi shekel 250, shekel 250 na turaren wuta mai ƙanshi,

  3. shekel 500 na kashiya, duk bisa ga ma’aunin shekel na tsattsarkan wuri, da moɗa na man zaitun.

  4. Da waɗannan za ka yi man shafewa mai tsarki, yadda mai yin turare yake yi. Zai zama man shafewa mai tsarki.

  5. Ka faɗa wa Isra’ilawa, ‘Wannan mai, zai zama mai tsarki ne a gare ni don shafewa, daga tsara zuwa tsara.

  6. Kada a zuba a jikunan mutane, kada kuma a yi wani mai irinsa. Wannan mai, mai tsarki ne, za ku kuma ɗauke shi a matsayi mai tsarki.

  7. Duk wanda ya yi irin wannan mai, duk wanda kuma ya shafa shi a kan wani wanda yake ba firist ba, za a ware shi daga mutanensa.’ ”