Skip to content

Ayoyin Littafi Mai Tsarki game da Agriculture

5 ayoyi · 2 fannoni

Mahimman ayoyin Littafi Mai Tsarki

  1. Ubangiji Allah ya ɗauko mutumin ya sa shi cikin Lambun Eden domin yă nome shi, yă kuma lura da shi.

  2. Da zuffan goshinka za ka ci abincinka har ka koma ga ƙasa, da yake daga cikinta aka yi ka. Gama kai turɓaya ne, kuma ga turɓaya za ka koma.”

  3. Saboda haka Ubangiji Allah ya kore shi daga Lambun Eden domin yă nome ƙasa wadda aka yi shi.

  4. Ba sa faɗa wa kansu, ‘Bari mu ji tsoron Ubangiji Allahnmu, wanda yake ba mu ruwan sama a kan kari na kaka da na bazara, wanda kullum yake tabbatar mana da girbi.’

  5. Ba ta yarda cewa ni ne wanda ya ba ta hatsi, sabon ruwan inabi da mai ba, wanda ya jibge mata azurfa da zinariya, waɗanda suka yi amfani wa Ba’al ba.