Skip to content

Memphis

8 verses · 2 known names

An kuma san shi da: Noph

29.8400, 31.2500 Duba a Google Maps

Ayoyin da suka ambaci Memphis

  1. Shugabannin Zowan sun zama wawaye, an ruɗe shugabannin Memfis dutsen kan kusurwa na mutanenta su sa Masar ta kauce.

  2. Haka ma, mutanen Memfis da Tafanes sun aske rawanin kanka

  3. Wannan maganata zo wa Irmiya game da dukan Yahudawa masu zama a Masar ta Ƙasa, a Migdol, Tafanes da Memfis, da kuma a Masar ta Bisa.

  4. “Ka yi shelar wannan a Masar, ka kuma furta shi a Migdol; ka yi shelarsa kuma a Memfis da Tafanes. ‘Ku ɗauki matsayinku ku kuma shirya, gama takobi na cin waɗanda suke kewaye da ku.’

  5. Ku tattara kayanku don shirin zuwa zaman bauta, ku da kuke zama a Masar, gama Memfis za tă zama kufai ta zama kango, babu mazauna.

  6. “ ‘Ga abin da Ubangiji Mai Iko Duka yana cewa, “ ‘Zan hallaka gumaka in kuma kawo ƙarshen siffofi a Memfis. Ba za a ƙara samun yerima a ƙasar Masar ba, zan kuma baza tsoro a duk fāɗin ƙasar.

  7. Zan ƙuna wuta wa Masar; Felusiyum za tă sha azaba mai zafi. Za a tayar wa Tebes da hankali; Memfis za tă riƙa kasance cikin ɓacin rai.

  8. Ko da sun kuɓuta daga hallaka, Masar za tă tattara su, Memfis kuma za tă binne su. Sarƙaƙƙiya za tă mamaye kayan azurfansu, ƙayayyuwa su tsiro a cikin tentunansu.