Skip to content

Baruch

21 ayoyi · 2 'yan gida

Ayoyin da suka ambaci Baruch

  1. na kuma ba wa Baruk ɗan Neriya, ɗan Masehiya, wannan takarda a gaban Hananel yaron ɗan’uwan mahaifina da kuma a gaban shaidun da suka sa hannu a takardan ciniki da kuma a gaban dukan Yahudawan da suke zaune a sansanin matsaran.

  2. “A gabansu na yi wa Baruk waɗannan umarnai cewa,

  3. “Bayan na ba da takardun ciniki ga Baruk ɗan Neriya, sai na yi addu’a ga Ubangiji na ce,

  4. Saboda haka Irmiya ya kira Baruk ɗan Neriya, yayinda Irmiya yake fadar dukan waɗannan maganganun da Ubangiji ya faɗa masa, Baruk ya rubuta su a littafin.

  5. Sai Irmiya ya ce wa Baruk, “An hana ni, ba zan tafi haikalin Ubangiji ba.

  6. Sai Baruk ɗan Neriya ya yi dukan abin da annabi Irmiya ya ce ya yi; a haikalin Ubangiji kuwa ya karanta maganar Ubangiji daga littafin

  7. Daga ɗakin Gemariya ɗan Shafan magatakarda, wanda yake a fili na bisa a mashigin Sabuwar Ƙofar haikali, Baruk ya karanta wa dukan mutane a haikalin Ubangiji maganar Irmiya daga littafin.

  8. Bayan Mikahiya ya faɗa musu kome da ya ji Baruk ya karanta wa mutane daga littafin,

  9. sai dukan fadawan suka aiki Yehudi ɗan Netaniya, ɗan Shelemiya, ɗan Kushi, ya ce wa Baruk, “Ka zo tare da littafin da ka karanta wa mutane.” Saboda haka Baruk ɗan Neriya ya tafi wurinsu tare da littafin a hannunsa.

  10. Suka ce masa, “Zauna, ka karanta mana littafin.” Sai Baruk ya karanta musu littafin.

  11. Da suka ji dukan maganar, sai suka dubi juna a firgice suka ce wa Baruk, “Dole mu sanar da dukan maganan nan ga sarki.”

  12. Sa’an nan suka ce wa Baruk, “Faɗa mana yadda ka yi ka rubuta dukan wannan. Irmiya ne ya yi maka shibtar ta?”

  13. Baruk ya amsa ya ce, “I, shi ne ya faɗa mini dukan wannan magana, na kuwa rubuta su a takarda.”

  14. Sa’an nan fadawan suka ce wa Baruk, “Kai da Irmiya ku je ku ɓuya. Kada ku bari wani ya san inda kuke.”

  15. A maimakon haka, sai sarki ya umarci Yerameyel ɗan sarki, Serahiya ɗan Azriyel da Shelemiya ɗan Abdeyel su kama Baruk marubuci da Irmiya annabi. Amma Ubangiji ya ɓoye su.

  16. Bayan sarki ya ƙone littafin da ya ƙunshi maganar da Baruk ya rubuta daga shibtar Irmiya, sai maganar Ubangiji ta zo wa Irmiya cewa,

  17. Sai Irmiya ta ɗauko wani littafi ya ba wa Baruk ɗan Neriya marubuci, kuma yayinda Irmiya yake shibtawa, Baruk ya rubuta a littafin dukan maganar da take a littafin da Yehohiyakim sarkin Yahuda ya ƙone. Ya kuma ƙara ire-iren maganganun nan a kansu.

  18. Amma Baruk ɗan Neriya yana zuga ka a kanmu don ka ba da mu ga Babiloniyawa, don su kashe mu ko su kai mu zaman bauta a Babilon.”

  19. Suka kuma kwashe dukan maza, mata da yara da ’ya’yan sarki mata waɗanda Nebuzaradan shugaban matsaran sarki ya bari tare da Gedaliya ɗan Ahikam, ɗan Shafan, da Irmiya annabi da kuma Baruk ɗan Neriya.

  20. Ga abin da Irmiya annabi ya faɗa wa Baruk ɗan Neriya a shekara ta huɗu ta Yehohiyakim ɗan Yosiya sarkin Yahuda, bayan Baruk ya rubuta maganar da Irmiya ya shibta masa a kan littafi cewa,

  21. “Ga abin da Ubangiji, Allah na Isra’ila, yana ce maka, Baruk.