Zabura 67
Addu’ar neman albarka da hasken Allah 1–2
1
Don mai bi da kaɗe-kaɗe. Tare da kayan kiɗi masu tsirkiya. Zabura. Waƙa. Bari Allah yă yi mana alheri yă kuma albarkace mu yă kuma sa fuskarsa ta haskaka a kanmu, Sela
2
don a san hanyoyinka a duniya, cetonka kuma a cikin dukan al’ummai.
Kira ga al’ummai su yabi Allah 3–5
3
Bari mutane su yabe ka, ya Allah; bari dukan mutane su yabe ka.
4
Bari al’ummai su yi murna su kuma rera don farin ciki, gama kana mulkin mutanenka da adalci kana kuma bi da al’umman duniya. Sela
5
Bari mutane su yabe ka, ya Allah; bari dukan mutane su yabe.
Amfanin albarkar Allah 6–7
6
Sa’an nan ƙasa za tă ba da girbinta Allah kuma, Allahnmu, zai albarkace mu.
7
Allah yă sa mana albarka, dukan iyakar duniya kuma su ji tsoronsa.
Rubutun Littafi Mai Tsarki: Biblica® Open Hausa Contemporary Bible™, © 2009, 2020 Biblica, Inc. · CC BY-SA 4.0“Biblica” is a trademark registered in the United States Patent and Trademark Office by Biblica, Inc., used with permission.
Study note