Skip to content

Zabura137

1
A bakin kogunan Babilon muka zauna muka yi kuka sa’ad da muka tuna da Sihiyona.
2
A can a kan rassan itatuwa muka rataye garayunmu,
3
gama a can masu kamunmu suka sa mu yi waƙoƙi, masu ba mu azaba suka nema waƙoƙin farin ciki; suka ce, “Ku rera mana ɗaya daga cikin waƙoƙin Sihiyona!”
4
Yaya za mu rera waƙoƙin Ubangiji a baƙuwar ƙasa?
5
In na manta da ke, ya Urushalima, bari hannuna na dama manta da iyawarsa.
6
Bari harshena yă manne wa rufin bakina in ban tuna da ke ba, in ban so Urushalima farin cikin mafi girma ba.
7
Ka tuna, ya Ubangiji, abin da mutanen Edom suka yi a ranar da Urushalima ta fāɗi. Suka yi ihu suka ce, “A ragargaza ta, A ragargaza ta har tushenta!”
8
Ya Diyar Babilon, an ƙaddara ke zuwa hallaka, mai farin ciki ne wanda ya sāka miki saboda abin da kika yi mana,
9
shi da ya ƙwace jariranki ya fyaɗa su a kan duwatsu.
Use arrow keys to navigate
Settings

Reading Style

Typeface

Font Size 19px

Options