Skip to content
Zakariya 4:1-7

Zakariya 4:1-7

1
Sai mala’ikan da ya yi magana da ni ya komo ya farkar da ni, kamar yadda ake farkar da mutum daga barcinsa.
2
Ya tambaye ni ya ce, “Me ka gani?” Na amsa, na ce, “Na ga wurin ajiye fitilan zinariya da kwano a kai, da kuma fitilu bakwai a kansa, da butocin kai wa fitilu mai guda bakwai.
3
Akwai kuma itatuwan zaitun guda biyu a gefensa, ɗaya a gefen dama na kwanon ɗaya kuma a gefen hagunsa.”
4
Na tambayi mala’ikan da ya yi magana da ni na ce, “Mene ne waɗannan, ranka yă daɗe?”
5
Sai ya amsa ya ce, “Ba ka san mene ne waɗannan ba?” Na amsa, na ce, “A’a, ranka yă daɗe.”
6
Sai ya ce mini, “Wannan ce maganar Ubangiji ga Zerubbabel. ‘Ba ta wurin ƙarfi ba, ko ta wurin iko, sai dai ta wurin Ruhuna,’ in ji Ubangiji Maɗaukaki.
7
“Kai mene ne, ya babban dutse? A gaban Zerubbabel za a rushe ka ka zama fili. Sa’an nan Zerubbabel yă kawo dutsen da ya fi kyau, a kuma yi ta sowa ana cewa, ‘Allah yă yi masa albarka! Allah yă yi masa albarka!’ ”
Settings

Reading style

Typeface

Font size 19px

Reading width 75 chars

Options