Skip to content
Titus 2:10

Titus 2:10

Ana nuna aya 10 tare da mahallin da ke kewaye.
7
Cikin kowane abu ka zama musu misali mai kyau ta wurin aikata abin da yake nagari. A cikin koyarwarka ka nuna mutunci da ƙwazo
8
da kuma sahihanci cikin maganar da ba za a iya kushewa ba, domin masu gāba da kai su ji kunya, su kuma rasa wani mugun abin da za su faɗa game da mu.
9
Ka koya wa bayi su yi wa iyayengijinsu biyayya cikin kowane abu, su yi ƙoƙari su gamshe su, kada su mayar musu da magana,
10
kada kuma su yi musu sata, sai dai su nuna za a iya amince da su sosai, don ta kowace hanya su sa koyarwa game da Allah Mai Cetonmu ta zama abin ɗaukan hankali.
11
Gama alherin Allah mai kawo ceto ya bayyana ga dukan mutane.
12
Yana koya mana mu ce, “A’a” ga rashin tsoron Allah da kuma sha’awace-sha’awacen duniya, mu kuma yi rayuwa ta kamunkai, ta adalci da kuma ta tsoron Allah a cikin wannan zamani,
13
yayinda muke sauraron begenmu mai albarka bayyanuwar ɗaukakar Allahnmu mai girma da kuma Mai Cetonmu, Yesu Kiristi,
Settings

Reading style

Typeface

Font size 19px

Reading width 75 chars

Options