Waƙar Waƙoƙi 8:8-14
8
Muna da ƙanuwa, nonanta ba su riga sun yi girma ba. Me za mu yi da ƙanuwarmu a ranar da za a yi maganar sonta?
9
Da a ce ita katanga ce, da sai mu gina hasumiyar azurfa a kanta. Da a ce ita ƙofa ce, da sai mun yi mata ƙyauren itacen al’ul.
10
Ni katanga ce kuma nonaina sun yi kamar hasumiya. Ta haka na zama idanunsa kamar wanda yake kawo gamsuwa.
11
Solomon ya kasance da gonar inabi a Ba’al-Hamon; ya ba da hayar gonar inabi ga ’yan haya. Kowanne zai biya shekel dubu na azurfa don ’ya’yan inabin.
12
Amma gonar inabina nawa ne da zan bayar; shekel dubu naka ne, ya Solomon, kuma ɗari biyu na waɗanda suke lura da ’ya’yan itatuwansa ne.
13
Ke da kike zaune a cikin lambu da ƙawaye suna lura da ke, bari in ji muryarki!
14
Ka zo, ƙaunataccena, ka zama kamar barewa ko kuwa kamar ’yar batsiya a kan dutsen da kayan yaji suke a shimfiɗe.
Settings