Waƙar Waƙoƙi 5:2-6
2
Na yi barci amma zuciyata tana a farke. Ku saurara! Ƙaunataccena yana ƙwanƙwasa ƙofa. “Buɗe mini, ’yar’uwata, ƙaunatacciyata, kurciyata, marar laifina. Kaina ya jiƙe da raɓa, gashina ya yi danshin ɗiɗɗigar dare.”
3
Na tuɓe rigata, sai in sāke sa ta kuma? Na wanke ƙafafuna, sai in sāke ɓata su?
4
Ƙaunataccena ya turo hannunsa ta cikin ramin ƙofar; zuciyata ta fara juyayi a kansa.
5
Na tashi don in buɗe wa ƙaunataccena, sai hannuna ya jiƙe sharkaf da mur, yatsotsina suna ɗiga da mur, a hannuwan ƙofar.
6
Na buɗe wa ƙaunataccena ƙofa, amma ƙaunataccena ba ya nan, ya riga ya tafi. Zuciyata ta damu da tafiyarsa. Na neme shi amma ban same shi ba. Na yi ta kiransa amma bai amsa ba.
Settings