Waƙar Waƙoƙi 3:1-4
1
Dare farai a kan gadona na nemi wanda zuciyata take ƙauna; na neme shi amma ban same shi ba.
2
Zan tashi yanzu in zagaya gari, in ratsa titunansa da dandalinsa; zan nemi wanda zuciyata take ƙauna. Saboda haka na neme shi, amma ban same shi ba.
3
Masu tsaro suka gamu da ni yayinda suke kai kawo a cikin birni, sai na ce, “Kun ga mini wanda zuciyata take ƙauna?”
4
Rabuwata da su ke nan sai na sami wanda zuciyata take ƙauna. Na riƙe shi, ban yarda yă tafi ba sai da na kawo shi gidan mahaifiyata, zuwa ɗakin wadda ta yi cikina.
Settings