Skip to content
Rut 1:7-18

Rut 1:7-18

7
Tare da surukanta biyu suka bar inda suka zauna suka kuma kama hanya da za tă komar da su zuwa ƙasar Yahuda.
8
Sai Na’omi ta ce wa surukanta biyu, “Ku koma, kowannenku, zuwa gidan mahaifiyarta. Bari Ubangiji yă nuna muku alheri yadda kuka nuna wa matattun nan da kuma gare ni.
9
Bari Ubangiji yă sa kowannenku ta sami hutu a gidan wani miji.” Sa’an nan ta sumbace su suka kuma yi kuka da ƙarfi
10
suka ce mata, “Za mu tafi tare da ke zuwa ga mutanenki.”
11
Amma Na’omi ta ce, “Ku koma gida, ’ya’yana mata. Don me za ku tafi tare da ni? Zan ƙara samun waɗansu ’ya’ya maza da za su zama mazanku ne?
12
Ku koma gida ’ya’yana mata; na tsufa ainun da zan sāke samun wani miji. Ko ma na yi tsammani har yanzu ina da bege, ko ma na sami miji a wannan dare na kuma haifi ’ya’ya maza,
13
za ku jira sai sun yi girma? Za ku ci gaba da kasance babu aure saboda su? A’a, ’ya’yana mata. Ina da baƙin ciki ƙwarai fiye da ku, domin hannun Ubangiji ya yi gāba da ni!”
14
A kan wannan suka sāke ɓarke da kuka. Sa’an nan Orfa ta sumbaci surukarta ta yi bankwana, amma Rut ta manne mata.
15
Sai Na’omi ta ce, “Duba, ’yar’uwanki ta koma zuwa ga mutanenta da kuma allolinta. Ki koma tare da ita.”
16
Rut Amma Rut ta amsa, “Kada ki roƙe ni in bar ki ko in koma daga gare ki. Inda za ki, zan tafi, kuma inda za ki zauna, zan zauna. Mutanenki, za su zama mutanena kuma Allahnki, zai zama Allahna.
17
Inda za ki mutu zan mutu, zan mutu a can kuma za a binne ni. Bari Ubangiji ya hukunta ni da tsanani sosai, in wani abu in ba mutuwa ce ta raba ke da ni ba.”
18
Sa’ad da Na’omi ta gane cewa Rut ta ƙudura tă tafi tare da ita, sai ta daina nema tă koma.
Settings

Reading Style

Typeface

Font Size 19px

Options