Skip to content
Rut 1:1-2

Rut 1:1-2

1
A kwanakin da mahukunta suke mulki an yi yunwa a ƙasar, sai wani mutum daga Betlehem a Yahuda tare da matarsa da ’ya’yansu maza biyu, suka tafi su yi zama na ɗan lokaci a ƙasar Mowab.
2
Sunan mutumin, Elimelek ne, sunan matarsa Na’omi; sunayen ’ya’yan nan nasu biyu, su ne Malon da Kiliyon. Su Efratawa ne daga Betlehem ta Yahuda. Suka kuwa tafi Mowab suka zauna a can.
Settings

Reading Style

Typeface

Font Size 19px

Options