Romawa 9:10-16
10
Ba ma haka kaɗai ba, ’ya’yan Rifkatu suna da mahaifi guda ne, wato, mahaifinmu Ishaku.
11
Duk da haka, tun ba a haifi tagwayen nan ba, balle su yi wani abu mai kyau ko marar kyau don nufin Allah bisa ga zaɓensa ya tabbata, ba ga aikin lada ba, sai dai ga kiransa,
12
ba ta wurin ayyuka ba sai dai ta wurin shi wanda ya kira, aka faɗa mata cewa, “Babban zai bauta wa ƙaramin.”
13
Kamar yadda yake a rubuce cewa, “Yaƙub ne na so, amma Isuwa ne na ƙi.”
14
Me za mu ce ke nan? Allah marar adalci ne? Sam, ko kaɗan!
15
Gama ya ce wa Musa, “Zan nuna jinƙai ga wanda zan nuna jinƙai, zan kuma ji tausayin wanda zan ji tausayi.”
16
Saboda haka, bai danganta ga sha’awar mutum ko ƙoƙarinsa ba, sai dai ga jinƙan Allah.
Settings