Skip to content
Romawa 8:1-8

Romawa 8:1-8

1
Saboda haka, yanzu babu hukunci don waɗanda suke cikin Kiristi Yesu,
2
gama ta wurin Kiristi Yesu dokar Ruhu mai ba da rai ta ’yantar da ni daga Dokar Musa.
3
Gama abin da dokar ba tă iya yi saboda kāsawar mutuntaka ba, Allah ya yi shi sa’ad da ya aiko da Ɗansa a kamannin mutum mai zunubi, don yă zama hadaya ta zunubi. Ta haka, ya hukunta zunubi a cikin mutum mai zunubi.
4
Ya yi haka domin yă cika bukatun adalcin doka a cikinmu, mu da ba ma rayuwa bisa ga mutuntaka, sai dai bisa ga Ruhu.
5
Waɗanda suke rayuwa bisa ga mutuntaka sun kafa hankulansu a kan sha’awace-shawa’acen jiki; amma waɗanda suke rayuwa bisa ga Ruhu sun kafa hankulansu a kan abubuwan da Ruhu yake so.
6
Ƙwallafa rai ga al’amuran halin mutuntaka ƙarshensa mutuwa ne, ƙwallafa rai ga al’amuran Ruhu kuwa rai ne da salama;
7
hankalin mai zunubi na gāba da Allah. Ba ya biyayya da dokar Allah, ba kuwa zai iya yin haka ba.
8
Waɗanda mutuntaka yake mulkinsu ba za su iya su gamshi Allah ba.
Settings

Reading Style

Typeface

Font Size 19px

Options