Ru’uya ta Yohanna 6:12-17
12
Ina kallo yayinda ya buɗe hatimi na shida. Sai aka yi babban girgizar ƙasa. Rana ta zama baƙa kamar gwado na gashin akuya, wata kuma gaba ɗaya ya zama ja wur kamar jini,
13
taurarin sararin sama suka fāffāɗi a ƙasa, kamar yadda ɗanyun ’ya’yan ɓaure suke fāɗuwa daga itacen ɓaure sa’ad da iska mai ƙarfi ta jijjiga shi.
14
Sararin sama kuwa ya janye kamar naɗaɗɗen littafi, ya yi ta naɗewa, aka kuma kawar da kowane dutse da kowane tsibiri daga wurinsa.
15
Sa’an nan sarakunan duniya, hakimai, jarumawa, masu arziki, masu ƙarfi, da kowane bawa da kuma kowane ’yantacce ya ɓoye a cikin koguna da kuma cikin duwatsun tsaunuka.
16
Suka kira duwatsu da tsaunuka suna cewa, “Ku fāɗi a kanmu ku kuma ɓoye mu daga fuskar wannan mai zama a kan kursiyi da kuma daga fushin Ɗan Ragon nan!
17
Gama babbar ranar fushinsu ta zo, wa kuwa zai iya tsayawa?”
Settings