Skip to content
Ru’uya ta Yohanna 5:9-14

Ru’uya ta Yohanna 5:9-14

9
Suka rera sabuwar waƙa, “Ka cancanci ka karɓi naɗaɗɗen littafin ka kuma buɗe hatimansa, domin an kashe ka, da jininka kuma ka sayi mutane wa Allah, daga kowace kabila da harshe da mutane da kuma al’umma.
10
Ka mai da su masarauta da kuma firistoci, don su yi wa Allahnmu hidima, kuma za su yi mulki a duniya.”
11
Sai na duba na kuma ji muryar mala’iku masu yawa, yawansu kuwa ya kai dubu dubbai, da kuma dubu goma sau dubu goma. Suka kewaye kursiyin da halittu huɗun nan masu rai da kuma dattawan nan.
12
Da babbar murya suka rera, “Macancanci ne Ɗan Ragon nan da aka kashe, don yă sami iko da wadata da hikima da ƙarfi da girma da ɗaukaka da kuma yabo!”
13
Sa’an nan na ji kowace halitta a sama da ƙasa da ƙarƙashin ƙasa da kuma bisan teku, da kome da yake cikinsu yana rerawa, “Gare shi mai zama a kan kursiyin da kuma ga Ɗan Ragon yabo da girma da ɗaukaka da iko,
14
Sai halittu huɗun nan masu rai suka ce, “Amin”, dattawan kuma suka fāɗi suka yi sujada.
Settings

Reading Style

Typeface

Font Size 19px

Options