Ru’uya ta Yohanna 3:19-22
19
Waɗanda nake ƙauna su nake tsawata wa, nake kuma horo. Saboda haka ka yi himma ka tuba.
20
Ga ni! Ina tsaye a bakin ƙofa, ina ƙwanƙwasawa. Duk wanda ya ji muryata ya kuma buɗe ƙofar, zan shiga in kuma ci tare da shi, shi kuma tare da ni.
21
Duk wanda ya ci nasara, zan ba shi ikon zama tare da ni a kursiyina, kamar yadda na ci nasara, kuma ina zaune tare da Ubana a kursiyinsa.
22
Duk mai kunnen ji, yă ji abin da Ruhu yake faɗa wa ikkilisiyoyi.”
Settings