Ru’uya ta Yohanna 21:12-14
12
Yana da babbar katanga mai tsayi, mai ƙofofi goma sha biyu, da kuma mala’iku goma sha biyu a ƙofofin. A bisa ƙofofin an rubuta sunayen kabilu goma sha biyu na Isra’ila.
13
Akwai ƙofofi uku a gabas, uku a arewa, uku a kudu, uku kuma a yamma.
14
An gina katangar birnin a kan tushen gini goma sha biyu, a kansu kuwa akwai sunayen manzannin sha biyu na Ɗan Ragon.
Settings