Skip to content
Ru’uya ta Yohanna 10:8-11

Ru’uya ta Yohanna 10:8-11

8
Sai muryar da na ji daga sama ta sāke magana da ni ta ce, “Tafi, ka karɓi naɗaɗɗen littafin da yake a buɗe a hannun mala’ikan da yake tsaye bisa teku da ƙasa.”
9
Sai na je wajen mala’ikan na ce masa yă ba ni ƙaramin naɗaɗɗen littafin. Ya ce mini, “Karɓa ka ci. Zai sa cikinka yă yi tsami, amma ‘a bakinka zai zama da zaƙi kamar zuma.’ ”
10
Na karɓi ƙaramin naɗaɗɗen littafin daga hannun mala’ikan na kuma ci. Ya yi zaƙi kamar zuma a bakina, amma sa’ad da na cinye, cikina ya yi tsami.
11
Sa’an nan aka ce mini, “Dole ne ka sāke yin annabci game da mutane masu yawa, al’ummai, harsuna da kuma sarakuna.”
Settings

Reading Style

Typeface

Font Size 19px

Options