Skip to content
Zabura 78:56-67

Zabura 78:56-67

56
Amma suka gwada Allah suka tayar wa Mafi Ɗaukaka; ba su kiyaye ƙa’idodinsa ba.
57
Kamar kakanninsu suka zama marasa biyayya da marasa aminci, marar tabbas kamar tanƙwararren baka.
58
Suka ba shi haushi da masujadansu na kan tudu; suka tayar da kishinsa da gumakansu.
59
Sa’ad da Allah ya ji su, ya yi fushi ƙwarai; ya ƙi Isra’ila gaba ɗaya.
60
Ya yashe tabanakul na Shilo, tentin da ya kafa a cikin mutane.
61
Ya aika da akwatin alkawarin ƙarfinsa zuwa bauta, darajarsa zuwa cikin hannuwan abokin gāba.
62
Ya ba da mutanensa ga takobi; ya yi fushi ƙwarai da gādonsa.
63
Wuta ta cinye matasansu maza, ’yan matansu kuma ba su da waƙoƙin aure;
64
aka karkashe firistocinsu, gwaurayensu kuwa ba su iya makoki ba.
65
Sa’an nan Ubangiji ya farka sai ka ce daga barcinsa, kamar yadda mutum kan farka daga buguwar ruwan inabi.
66
Ya kori abokan gābansa; ya sa suka sha madawwamiyar kunya.
67
Sa’an nan ya ƙi tentunan Yusuf, bai zaɓi kabilar Efraim ba;
Settings

Reading Style

Typeface

Font Size 19px

Options