Zabura 78:56-64
56
Amma suka gwada Allah suka tayar wa Mafi Ɗaukaka; ba su kiyaye ƙa’idodinsa ba.
57
Kamar kakanninsu suka zama marasa biyayya da marasa aminci, marar tabbas kamar tanƙwararren baka.
58
Suka ba shi haushi da masujadansu na kan tudu; suka tayar da kishinsa da gumakansu.
59
Sa’ad da Allah ya ji su, ya yi fushi ƙwarai; ya ƙi Isra’ila gaba ɗaya.
60
Ya yashe tabanakul na Shilo, tentin da ya kafa a cikin mutane.
61
Ya aika da akwatin alkawarin ƙarfinsa zuwa bauta, darajarsa zuwa cikin hannuwan abokin gāba.
62
Ya ba da mutanensa ga takobi; ya yi fushi ƙwarai da gādonsa.
63
Wuta ta cinye matasansu maza, ’yan matansu kuma ba su da waƙoƙin aure;
64
aka karkashe firistocinsu, gwaurayensu kuwa ba su iya makoki ba.
Settings