Zabura 78:1-8
1
Maskil na Asaf. Ya mutanena, ku ji koyarwata; ku saurari kalmomin bakina.
2
Zan buɗe bakina da misalai, zan faɗi ɓoyayyun abubuwa, abubuwan dā,
3
abin da muka ji muka kuma sani, abubuwan da kakanninmu suka faɗa mana.
4
Ba za mu ɓoye su wa ’ya’yanmu ba; za mu faɗa wa tsara mai zuwa ayyukan da suka zama yabo na Ubangiji, ikonsa, da abubuwan banmamakin da ya aikata.
5
Ya kafa ƙa’idodi wa Yaƙub ya kuma kafa doka a cikin Isra’ila, wadda ya umarce kakanni-kakanninmu su koya wa ’ya’yansu,
6
don tsara na biye su san su, har da ’ya’yan da ba a riga an haifa ba, su kuma su faɗa wa ’ya’yansu.
7
Ta haka za su dogara ga Allah ba kuwa za su manta da ayyukansa ba amma za su kiyaye umarnansa.
8
Ba za su zama kamar kakanni kakanninsu ba, masu taurinkai da kuma tsara masu tayarwa, waɗanda zukatansu ba su yi biyayya ga Allah ba, waɗanda zukatansu ba su yi aminci ga Allah ba.
Settings