Zabura 62:1-4
1
Don mai bi da kaɗe-kaɗe. Don Yedutun. Zaburar Dawuda. Raina na samun hutu a wurin Allah ne kaɗai; cetona na zuwa daga gare shi.
2
Shi kaɗai ne dutsena da cetona; shi ne kagarata, ba zan jijjigu ba.
3
Har yaushe za ku tasar wa mutum guda? Dukanku ne za ku kā da shi wannan jinganannen bango, wannan rusasshen katanga?
4
Sun kintsa sosai su tumɓuke shi daga matsayinsa mai martaba; suna jin daɗi yin ƙarairayi. Sukan sa wa mutum albarka da bakinsu, amma a zuciyarsu la’antawa suke yi. Sela
Settings