Zabura 40:3-6
3
Ya sa sabuwar waƙa a bakina, waƙar yabo ga Allahna. Da yawa za su gani su tsorata su kuma dogara ga Ubangiji.
4
Mai albarka ne mutumin da ya mai da Ubangiji abin dogararsa, wanda ba ya kula da masu girman kai, waɗanda suka juya ga allolin ƙarya.
5
Da yawa ne, ya Ubangiji Allahna, abubuwan banmamakin da ka aikata. Abubuwan da ka shirya mana. Ba wanda zai iya faɗa maka su; a ce zan yi magana in faɗe su, za su wuce gaban misali a furta.
6
Hadaya da sadaka ba ka sha’awa, amma kunnuwana ka huda; hadayun ƙonawa da hadayun zunubi ba ka bukata.
Settings