Zabura 40:1
Ana nuna aya 1 tare da mahallin da ke kewaye.
1
Don mai bi da kaɗe-kaɗe. Ta Dawuda. Zabura ce. Na jira da haƙuri ga Ubangiji; ya juya wurina ya kuma ji kukata.
2
Ya ɗaga ni daga rami marar fāɗi, daga laka da taɓo; ya sa ƙafafuna a kan dutse ya kuma ba ni tsayayyen wuri don in tsaya.
3
Ya sa sabuwar waƙa a bakina, waƙar yabo ga Allahna. Da yawa za su gani su tsorata su kuma dogara ga Ubangiji.
4
Mai albarka ne mutumin da ya mai da Ubangiji abin dogararsa, wanda ba ya kula da masu girman kai, waɗanda suka juya ga allolin ƙarya.
Settings