Skip to content
Zabura 36:1-4

Lalacewar mugaye

Zabura 36:1-4
1
Don mai bi da kaɗe-kaɗe. Ta Dawuda bawan Ubangiji. Akwai magana a cikin zuciyata game da zunubin mugu. Babu tsoron Allah a idanunsa.
2
Gama a idanunsa yana ganin kansa wani abu ne wanda ya sha ƙarfi a gane ko ya ƙi zunubinsa.
3
Kalmomin bakinsa mugaye ne da kuma ruɗu; ya daina zama mai hikima da yin alheri.
4
Ko a kan gadonsa ma yana shirya mugunta; yakan sa kansa ga aikata zunubi kuma ba ya ƙin abin da ba shi da kyau.

Rubutun Littafi Mai Tsarki: Biblica® Open Hausa Contemporary Bible™, © 2009, 2020 Biblica, Inc. · CC BY-SA 4.0“Biblica” is a trademark registered in the United States Patent and Trademark Office by Biblica, Inc., used with permission.