- English
- King James KJV
- Complete Jewish CJB
- World English WEBM
- Berean Standard BSB
- American Standard ASV
- Geneva GNV
- Young's Literal YLT
- Douay-Rheims DRC
- International
- Shqip ALB
- العربية SVD
- বাংলা BN-IRV
- မြန်မာ Judson
- 简体文 CUV-S
- 繁體中文 CUV-T
- Čeština BKR
- Nederlands STVE
- Français LSG
- Deutsch SCH
- Ελληνικά Vamvas
- ગુજરાતી GU-IRV
- Hausa HCB
- עברית Hebrew
- हिन्दी HCV
- Magyar KAROLI
- Bahasa Indonesia INDO-TB
- Italiano Diodati
- 日本語 Kougo
- 한국어 Korean
- മലയാളം MAL
- मराठी MRCV
- Norsk DNB
- فارسی OPV
- Polski BG
- Português Almeida
- Română Cornilescu
- Русский Synodal
- Español RVG
- Kiswahili Neno
- Svenska SV1917
- Tagalog TAG-ADB
- தமிழ் TCV
- తెలుగు TSA
- ภาษาไทย THAI-KJV
- Українська Ohienko
- Tiếng Việt CADMAN
- Yorùbá YCB
Zabura 33:13-18
13
Daga sama Ubangiji ya duba ya kuwa ga dukan ’yan adam;
14
daga mazauninsa yana lura da dukan waɗanda suke zama a duniya,
15
shi da ya yi zukatan duka, wanda yake kula da kome da suke yi.
16
Babu sarkin da ake ceto ta wurin yawan mayaƙansa; ba jarumin da kan kuɓuta ta wurin yawan ƙarfinsa.
17
Dogara a kan doki don ceto banza ne; duk da yawan ƙarfinsa ba ya ceto.
18
Amma idanun Ubangiji suna a kan wanda yake tsoronsa, a kan waɗanda suke sa zuciya cikin ƙaunarsa marar ƙarewa,
Nazarin nassin nan
Sharhi a kan nassin, ba aya ɗaya ba
- Su wane
- Ina
- Yaushe
- About
Sauran wuraren da Nassi ya faɗi haka
1 Bitrus 3:12
Gama idanun Ubangiji suna a kan masu adalci kunnuwansa kuma suna jin addu’arsu, amma fuskar Ubangiji tana gāba da masu mugunta.”daga aya ta 18Ayuba 36:7
Ba ya fasa duban masu adalci; yana sa su tare da sarakuna yana ɗaukaka su har abada.daga aya ta 18Zabura 147:11
Ubangiji yakan yi farin ciki a waɗanda suke tsoronsa, waɗanda suke sa zuciya a ƙaunarsa marar ƙarewa.daga aya ta 18Zabura 34:15
Idanun Ubangiji suna a kan masu adalci kuma kunnuwansa suna sauraran kukansu;daga aya ta 18Zabura 34:20
yakan tsare dukan ƙasusuwansa, ba ko ɗayansu da zai karye.daga aya ta 18Ayuba 28:24
Gama yana ganin iyakar duniya kuma yana ganin duk abin da yake ƙarƙashin sama.daga aya ta 13Karin Magana 21:31
Akan shirya doki domin ranar yaƙi, amma nasara tana ga Ubangiji ne.daga aya ta 17Ibraniyawa 6:18
Allah ba ya karya! Haka ma alkawuransa da rantsuwarsa abubuwa biyu ne da ba a iya canjawa. Mun gudu zuwa wurin Allah domin kāriya. Ya kamata alkawuransa su ƙarfafawa sosai mu riƙe begen nan da yake gabanmu.daga aya ta 18Zabura 11:4
Ubangiji yana cikin haikalinsa mai tsarki; Ubangiji yana a kursiyinsa a sama. Yana kallon ’ya’yan mutane; idanunsa suna bincike su.daga aya ta 13Irmiya 32:19
manufofinka da girma suke, ayyukanka kuma masu girma ne. Idanunka suna a buɗe ga dukan hanyoyin mutane; kakan sāka wa kowa gwargwadon halinsa yadda ya dace.daga aya ta 15Zabura 20:7
Waɗansu sun dogara a kekunan yaƙi waɗansu kuma a dawakai, amma mu, mun dogara a cikin sunan Ubangiji Allahnmu.daga aya ta 17Zabura 13:5
Amma na dogara a kan ƙaunarka marar ƙarewa; zuciyata tana farin ciki a cikin cetonka.daga aya ta 18
Bayanin Nazari
Settings