Zabura 33:1-11
1
Ku rera da farin ciki ga Ubangiji ku adalai; daidai ne masu gaskiya su yabe shi.
2
Ku yabi Ubangiji da garaya; ku yi kiɗi gare shi da molo mai tsirkiya goma.
3
Ku rera masa sabuwar waƙa; ku yi kiɗi da gwaninta, ku kuma yi sowa don farin ciki.
4
Gama maganar Ubangiji daidai ne da kuma gaskiya; yana da aminci cikin kome da yake yi.
5
Ubangiji yana ƙaunar adalci duniya ta cika da ƙaunarsa marar ƙarewa.
6
Ta wurin maganar Ubangiji aka yi sammai, rundunar taurarinsu kuwa da numfashin bakinsa.
7
Ya tattara ruwan teku cikin tuluna; ya sa zurfafa cikin gidajen ajiya.
8
Bari dukan duniya ta ji tsoron Ubangiji; bari dukan mutanen duniya su girmama shi.
9
Gama ya yi magana, abu ya kuwa kasance; ya umarta, ya kuwa tsaya daram.
10
Ubangiji yakan soke shirye-shiryen al’ummai; yakan wofintar da manufofin mutane.
11
Amma shirye-shiryen Ubangiji kan tsaya daram har abada, manufofin zuciyarsa kuwa har dukan zamanai.
Settings