Skip to content
Zabura 17:1-3

Zabura 17:1-3

Roƙon a yi shari’a da adalci

1
Addu’a ce ta Dawuda. Ka ji, ya Ubangiji, roƙona na adalci; ka saurari kukata. Ka kasa kunne ga addu’ata, ba ta fitowa daga leɓuna masu ƙarya.
2
Bari fiffitawata tă zo daga gare ka; bari idanunka su ga abin da yake daidai.
3
Ko ka duba zuciyata, ka kuma bincike ni da dare, ko ka gwada ni, ba za ka sami kome ba; na yanke shawara cewa bakina ba zai yi zunubi ba.

Nazarin nassin nan

Sharhi a kan nassin, ba aya ɗaya ba

Sauran wuraren da Nassi ya faɗi haka

  • Zabura 26:2

    Ka jarraba ni, ya Ubangiji, ka kuma gwada ni, ka bincike zuciyata da tunanina;
    daga aya ta 3
  • Ayyukan Manzanni 11:23

    Da ya iso ya kuma ga tabbacin alherin Allah, sai ya yi farin ciki ya kuma ƙarfafa su duka su tsaya da gaskiya cikin Ubangiji da dukan zukatansu.
    daga aya ta 3
  • Ayuba 23:10

    Amma ya san hanyar da nake bi; sa’ad da ya gwada ni zan fito kamar zinariya.
    daga aya ta 3
  • Zabura 39:1

    Don mai bi da kaɗe-kaɗe. Don Yedutun. Zabura ta Dawuda. Na ce, “Zan lura da hanyoyina zan kuma kiyaye harshena daga zunubi; zan sa linzami a bakina muddin mugaye suna a gabana.”
    daga aya ta 3
  • Zabura 142:6

    Ka saurari kukata, gama ina cikin matsananciyar bukata; ka cece ni daga waɗanda suke fafarata, gama sun fi ni ƙarfi sosai.
    daga aya ta 1
  • Malaki 3:2

    Amma wa zai jure wa ranar zuwansa? Wa zai iya tsaya sa’ad da ya bayyana? Gama zai zama kamar wuta mai tace ƙarfe, ko sabulu mai wanki.
    daga aya ta 3
  • Zabura 66:10

    Gama kai, ya Allah, ka gwada mu; ka tace mu kamar azurfa.
    daga aya ta 3
  • Zabura 119:106

    Na yi rantsuwa na kuma tabbatar da shi, cewa zan bi dokokinka masu adalci.
    daga aya ta 3
  • Zabura 139:1

    Don mai bi da kaɗe-kaɗe. Ta Dawuda. Zabura ce. Ya Ubangiji, ka bincike ni ka kuwa san ni.
    daga aya ta 3
  • Zakariya 13:9

    Wannan kashi ɗaya bisa ukun zan kawo in sa a cikin wuta; zan tace su kamar azurfa in gwada su kamar zinariya. Za su kira bisa sunana zan kuwa amsa musu; zan ce, ‘Su mutanena ne,’ za su kuma ce, ‘Ubangiji ne Allahnmu.’ ”
    daga aya ta 3
  • Zabura 61:1

    Don mai bi da kaɗe-kaɗe. Da kayan kiɗi masu tsirkiya. Ta Dawuda. Ka ji kukata, ya Allah; ka saurari addu’ata.
    daga aya ta 1
  • 1 Bitrus 1:7

    Wannan kuwa domin a tabbatar da sahihancin bangaskiyarku ne, wadda ta fi zinariya daraja nesa, ita zinariya kuwa, ko da yake mai ƙarewa ce, akan gwada ta da wuta, domin bangaskiyan nan taku ta jawo muku yabo da girma da ɗaukaka a bayyanar Yesu Kiristi.
    daga aya ta 3
Settings

Reading Style

Typeface

Font Size 19px

Options