Zabura 147:1-9
1
Yabi Ubangiji. Yana da kyau a rera yabai ga Allahnmu, abu mai daɗi ne daidai ne kuma a yabe shi!
2
Ubangiji ya gina Urushalima; ya tattara kamammu na Isra’ilan da aka kai bauta.
3
Ya warkar da masu raunanar zuciya ya ɗaɗɗaura miyakunsu.
4
Ya lissafta yawan taurari ya kuma kira kowannensu da suna.
5
Shugabanmu mai girma ne mai iko duka; ganewarsa ba shi da iyaka.
6
Ubangiji yana kula da masu sauƙinkai yakan yar da mugaye a ƙasa.
7
Rera wa Ubangiji waƙar godiya; ku kada garaya ga Allahnmu.
8
Ya rufe sararin sama da gizagizai; yana tanada wa duniya ruwan sama yana kuma sa ciyawa tă yi girma a kan tuddai.
9
Yakan tanada wa shanu abinci da kuma saboda ’ya’yan hankaki sa’ad da suka yi kira.
Settings