Skip to content
Zabura 119:113-120

SAMEK: Dogara ga Allah Mai Mafaka

Zabura 119:113-120
113
Na ƙi mutane masu baki biyu, amma ina ƙauna dokarka.
114
Kai ne mafakata da garkuwata; na sa zuciyata a maganarka.
115
Ku rabu da ni, ku masu aikata mugunta, don in kiyaye umarnan Allahna!
116
Ka raya ni bisa ga alkawarinka, zan kuwa rayu; kada ka bari a gwale sa zuciyata.
117
Ka riƙe ni za a kuma cece ni; kullayaumi zan ɗauka ƙa’idodinka da muhimmanci.
118
Ka ki dukan waɗanda suka kauce daga ƙa’idodinka, gama yaudararsu banza ne.
119
Dukan mugayen duniya ka zubar kamar datti; saboda haka nake ƙaunar farillanka.
120
Naman jikina na rawan jiki don tsoronka; na cika da tsoron dokokinka.

Rubutun Littafi Mai Tsarki: Biblica® Open Hausa Contemporary Bible™, © 2009, 2020 Biblica, Inc. · CC BY-SA 4.0“Biblica” is a trademark registered in the United States Patent and Trademark Office by Biblica, Inc., used with permission.